Ma'aikatan ExxonMobil na yin zanga-zanga kan zargi rage ma'aikata

Ana huda bututun mai a Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daya daga cikin kamfunonin da ke hakar mai a Nigeria

Ma'aikatan kamfanin mai na ExxonMobil sun rufe ofishin kamfanin da ke Legas, don nuna adawa da shirinsa na rage ma'aikata.

Ma'aikatan kamfanin sun fara zanga-zanga ne tun a ranar Laraba, bayan da kungiyar manyan mai da iskar gas ta Nigeria, PENGASSAN, ta bukace su yi hakan.

Kungiyar kwadagon ta zargi ExxonMobil da shirin sallamar ma'aikata sama da 100 ba tare da tattaunawa ko tuntubar ba.

Akwai fargabar cewa hakan zai shafi harkar samar da mai a kasar.

Hare-haren da mayakan sa-kai ke kaiwa ba kakkautawa dai sun rage yawan man da kasar ke fitarwa a kullum daga ganga miliyan biyu da rabi da dubu dari biyu.

Sai dai kuma har yanzu ExxonMobil bai ce komai ba game da zargin shirin sallamar ma'aikatan da ma zanga-zangar da ake yi.