An amince a haifi jarirai daga iyaye uku a Birtaniya

Haifar yara jarirai

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto,

An yi haka ne domin rage haifar yara da cututtuka

Hukumar Kula da Haihuwa ta Birtaniya ta yanke wata shawara mai cike da tarihi, wadda za ta bayar da damar haifar jarirai daga iyaye uku.

Yanzu asibitoci za su iya neman izini daga hukumar kula da haihuwar mutane, domin su yi amfani da fasahar da ake kira IVF, inda za a hada kwan mace da kuma maniyyin namiji a cikin mahaifar wata matar daban.

Wannan fasaha dai za ta hana haifar jarirai da cututtuka masu kisa, wadanda ke da nasaba da kwayoyin halittar gado.

A watan Disamban wannan shekara, wata tawagar likitocin Amurka, ta karbi haihuwar wani jariri mai dauke da kwayoyin halittar mutane uku a Mexico, ta hanyar amfani da wannan fasahar.