Majalisar dokokin Isra'ila ta amince mata su sanya guntun skel (skirt)

Masu zanga-zanga kan batun sun taru a ginin majalisar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga kan batun sun taru a ginin majalisar

Rahotanni sun ce majalisar dokokin Isra'ila ta dakatar da dokar da ta yi ta hana mata sanya guntun kamfai, wato skel bayan ma'aikata sun yi bore.

Ma'aikatan sun ce majalisar dokokin ta tsaurara kan tsayin kamfen da ya kamata a rika sanyawa, inda ta hana wasu ma'aikatan shiga ginin majalisar.

Sai dai kakakin majalisar Yuli Edelstein ya ce sun hana sanya guntayen skel ne saboda korafe-korafen da aka kai musu cewa mutane na yin shigar da bata dace ba.

Wani kwamitin hadin-gwiwa zai yi nazari kan dokar da zummar gyara ta.

Jaridar Haaretz ta kasar ta ce an dakatar da dokar ne bayan wasu taruka masu cike da ce-ce-ku-ce da aka gudanar kan batun a cikin majalisar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dokar ba ta iyakance tsawon skel din da za a sanya ba