Facebook ya dauki matakin hana watsa labaran ƙanzon-kurege

Mark Zuckerberg yana bayyana kansa a matsayin shugaban Facebook

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Facebook ya ce ba sa goyon bayan labaran karya

Kamfanin Facebook ya kaddamar da wasu sababbin matakai na hana watsa labaran ƙarya a shafinsa.

Sababbin matakan, wadanda za su zo tare da wasu sauye-sauye, za su tabbatar ba a rika watsa labaran da ba su da tushe ta hanyar Facebook ba.

Facebook ya sha suka sosai a watan jiya bayan wasu masu amfani da shi sun yi zargin cewa labaran karairayin da aka rika watsawa ta shafin sun yi tasiri a zaben da aka yi wa Donald Trump a matsayin shugaban Amurka.

Sababbin matakan za su hada da bai wa masu amfani da shafin damar jan hankalin Facebook idan suka ga labarai karya, tare da sauyi kan tsarin nuna labarai a Facebook.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce, "Mun yi amanna da bai wa mutane damar fadin albarkacin bakinsu kuma ba za mu zama masu kayyadewa mutane gaskiya ko karyar al'amari ba, don haka muna bin wannan matsala sannu a hankali."

Facebook ya kara da cewa ya samar da wani gurbi da zai bai wa masu amfani da shi zabi nuna labari "idan na bogi ne."

Haka kuma za a samar da alamar da za ta nuna idan labari mai "cike da ka-ce-na-ce ne" domin Facebook ya mika shi ga wadanda suka rubuta shi su sake tantance shi.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Facebookya fitar da sabbin hanyoyin kai rahoton labarin kanzon-kurege