Gwamnatin Syria ta dakatar da kwashe farar-hula daga Aleppo

Akalla mutum 6,000 sun fice daga gabashin Aleppo

Asalin hoton, GEORGE OURFALIAN

Bayanan hoto,

Akalla mutum 6,000 sun fice daga gabashin Aleppo

Gwamnatin Syria ta dakatar da kwashe farar-hula daga gabashin Aleppo, tana mai zargin 'yan tawaye da keta yarjejeniyar tsagaita bude wutar da suka sanyawa hannu.

Wasu majiyoyin gwamnati sun ce 'yan tawayen sun hana a fitar da farar-hula daga yankuna biyu da ke hannun gwamnati a wani bangaren na Syria, kamar yadda aka yi alkawari a yarjejeniyar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake cewa an bude wuta kan motocin da ke dauke da farar-hular da ke ficewa daga gabashin birnin.

An fitar da akalla mutum 6,000 ranar Alhamis daga Aleppo, amma majalisar dinkin duniya ta ce har yanzu akwai mutum 50,000 da suka rage a birnin.

Dakarun tsaron Syria, tare da goyon bayan Rasha, sun kwace kusan dukkan yankunan da ke hannun 'yan tawayew na gabashin Aleppo.

Ana samun rahotanni daban-daban kan dalilin da ya sa aka dakatar da kwashe farar-hula daga Aleppo.

Gidan talabijin din kasar ya ce 'yan tawayen sun yi yunkurin kama farar-hular da ake ficewa da su daga birnin.

Sai dai kuma wata kafar watsa labarai ta soji da ke goyon bayan gwamnati ta ce masu zanga-zanga sun toshe hanyoyin da ake bi domin fitar da farar-hula da mayaka daga gabashin birnin, inda suka bukatar a bar mutane su fice daga garuruwan Foua da Kefraya na lardin Idlib da ke hannun 'yan Shia - inda nan ne 'yan tawayen da ke hamayya da Shugaba Bashar al-Assad suka fi karfi.