Kotu ta yi watsi da bukatar Nyako kan komawa mulki

Nyako
Bayanan hoto,

Nyako ya sha kaye a kotun koli

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako kan ta mayar da shi kan kujerarsa domin ya karasa wa'adin mulkisa.

Majalisar dokin jihar Adamawa ce dai ta cire Nyako daga kan mulki a watan Yulin shekarar 2014 wata goma kafin ya kammala wa'adinsa.

'Yan majalisar sun tsige shi ne bisa abin da suka ce saba ka'idar aiki da almubazzaranci da dukiyar al'umma.

Da suka yin watsi da bukatar tasa, alkalai bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin mai sharia Tanko Muhammad sun amince da hukuncin kotun daukaka kara wanda ya ce tsigewar da aka yi wa Nyako bai dace ba, amma ba za ta mayar da shi kan mulki ba saboda yadda karamar kotu ta tafiyar da lamarin.

Sun kara da cewa lauyan Murtala Nyako ya yi kasassaba kan karar da ya shigar a kotun daukaka kara saboda bukatar da ya shigar a gabanta domin ya janye batun sake mayar da tsohon gwamnan kan kujerarsa.