Wasu daga cikin hotunan Afirka na wannan makon

Wasu daga cikin hotunan da muka samu daga yankunan Afirka daban-daban na wannan makon:

Wani saurayi ya yi daka-tsari a cikin ruwa ranar Asabar a fitaccen bakin tekun nan na Camps Bay da ke birnin Cape Town, na Afirka ta kudu yayin da ake fama da zafi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wani saurayi ya yi daka-tsari a cikin ruwa ranar Asabar a fitaccen bakin tekun nan na Camps Bay da ke birnin Cape Town, na Afirka ta kudu yayin da ake fama da zafi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ranar Juma'a, wani mutum ya jefa wannan yarinyar sama kafin ta shiga gasar rawa a cibiyar kula da al'adu ta Palais de la Culture da ke Abidjan, babban birnin Ivory Coast.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan mai wasan jifa da mashin ya shiga gasaR Olympics ta Maasai ranar Asabar a bangaren kungiyar Sidai Oleng ta Kenya. Ana yin gasar ne a kamfe din kare namun daji a al'umar Maasai.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A wurin gasar ne kuma aka yi wa wannan yarinyar kwalliya da jan fenti

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ranar lahadi a birnin Nairobi, fitaccen mawakin nan na Kenya Ayub Ogada, ya yi bikin wasa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranar Juma'a kuma, mawaka sun shanya tufafinsu bayan sun gama rawa a birnin Bamako na Mali

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranar Talata, wannan matar na sayar da kayayyaki domin bikin Kirsimeti a birnin Lagos na Najeriya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shi ma wannan yaron ya yi ado a lokacin bukukuwan Maulidi a birnin Benghazi na kasar Libya ranar Asabar..

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan yarinyar kuwa ta yi ado da abin rufe fuska domin bikin tunawa da ranar haihuwar manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) a birnin na Benghazi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wadannan masu son kwallon rugby din guda biyu sun yi shiga a matsayin Groot da Rocket Raccoon na cikin fim din Guardians of the Galaxy a a lokacin wasan da aka yi tsakanin Ingila da Scotland a Cape Town.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An jefa wannan babbar balan-balan din a saman Luxor ranar Talata, domin bai wa masu yawon bude ido abin da za su kashe kwarkwatar idanunsu a tsohon birnin na Masar.

Asalin hoton, EPA

Mun samu hotuna ne daga AFP, AP, EPA, Reuters