Tashin bama-bamai ya kashe mutane da dama a Turkiyya

Rahotanni sun ce bama-baman sun tashi a kiusa da wata mota

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Rahotanni sun ce bama-baman sun tashi a kiusa da wata mota

Jami'an tsaro sun ce mutane da dama ne suka mutu yayin da wasu kuma suka jikkata bayan wasu bama-bamai sun tashi a kusa da wata mota a tsakiyar birnin Kayseri na kasar Turkiyya.

Rahotanni sun ce motar na dauke da sojojin da suka tashi daga aiki, kuma tana kusa da wata jami'a a lokacin da bama-baman suka tashi.

Kamfanin dillancin labaran Dogan na kasar ta Turkiyya ya ce an dasa bama-baman ne a jikin motar.

Wannan lamari ya faru ne mako daya bayan wani harin bam ya kashe akalla mutum 44 a Istanbul, wanda mayakan Kurdawa suka dauki nauyin kai wa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Bas din ta kama da wuta

Hotunan da aka watsa a gidajen talabijin sun nuna motar bas din ta yi kaca-kaca.

Kasar Turkiyya dai ta yi fama da hare-haren bama-bama daga wajen Kurdawa da masu ikirarin jihadi a wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce ofishin firai ministan kasar Binali Yildirim ya sanya takunkumin hana 'yan jarida zuwa wajen da aka tayar da bama-baman na wani dan lokaci.

Ofishin ya umarci 'yan jarida da su guji wallafa duk wani labari da zai sanya "tsoro da fargaba a zukatan mutane, lamarin da zai sa 'yan ta'adda su ji tamkar bukatarsu ta biya".