Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe sojoji da dama a Yemen

Dakarun da ke goyon bayan gwamnati ne ke rike da birnin na Aden

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dakarun da ke goyon bayan gwamnati ne ke rike da birnin na Aden

Wani dan kunar-bakin-wake ya kashe sojoji akalla 23 kana ya jikkata wasu da dama bayan ya tayar da bama-baman da ke jikinsa a birnin Aden mai tasoshin jiragen ruwa na kasar Yemen.

Rahotanni sun ce sojojin na kan layin karbar albashi kusa da barikinsu lokacin da dan kunar-bakin-wake ya tayar da bama-baman.

Mutumin ya saje da sojojin ne a barikin Al-Solban da ke gundumar Al-Arish, a cewar jami'an soji.

Hakan na faruwa ne bayan da a farkon makon da muke ciki wasu tagwayen hare-hare da aka kai wa sojoji suka yi sanadin mutuwar 48 daga cikinsu.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na ranar Lahadi, sai dai masu ikirarin jihadi sun sha kai hare-hare a yankin.

A watan Agusta, wani harin kunar-bakin-wake da kungiyar IS ta yi ikirarin kai wa a wata cibiyar daukar sojoji aiki da ke birnin ya halaka akalla mutum 70.