Venezuela ta jinkirta sauya takardar kudinta

Masu zanga-zanga sun rika kona takardar kud ta 100-bolivar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun rika kona takardar kud ta 100-bolivar

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya jinkirta sauya babbar takardar kudin kasar 100-bolivar zuwa ranar biyu ga watan Janairu.

Dakatar da sauya takardar kudin da aka yi kwatsama na zuwa ne bayan kasar ta fada rudani ta fannin tattalin arziki.

A jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta gidan talabijin, Mr Maduro ya yi ikirarin cewa kasashen waje ne ke yi wa kasar zagon-kasa, lamarin da ya sa sabuwar takardar kudin 500-bolivar ba ta fara aiki ba.

'Yan kasar ta Venezuela sun shafe kwana da kwanaki a kan layuka domin su sauya tsofaffin takardun kudinsu da sababbin da za su fara aiki.

An rufe dubban kantuna saboda karancin kudi, kuma yawancin mutane sun dogara ne da yin amfani da katin cirar kudi ko kuma aika kudin ta intanet idan dai suna son yin saye da sayarwa.

Hasalima, lamarin ya sa mutane da dama ba sa iya sayen abinci.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa fushin da 'yan kasar ke yi kan matakin ya sa sun yi taho-mu-gama da jami'an tsaro a birane shida ranar Juma'a.

Ya kara da cewa lamarin ya kai ga kama mutum 32, sannan aka jikkata mutum guda.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana fasa shaguna, ciki har da wannan gidan biredin na Ciudad Bolivar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kasar Venezuela sun kwashi kayan abinci daga kantuna bayan an fasa su

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Nicolas Maduro ya ce soke 100-bolivar zai hana masu fasa-kwauri