Ana yin zaben 'yan majalisar dokokin Ivory Coast

Laurent Gbagbo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana yi wa Laurent Gbagbo shari'a bisa zargin aikata laifukan cin zarafin bil adama.

An aike da jami'an tsaro kusan 30,000 a yankuna daban-daban na Ivory Coast a yayin da ake zaben 'yan majalisar dokokin kasar ranar Lahadi.

Shugaba Alassane Ouattara ya yi kira ga 'yan kasar da su zabi jam'iyyarsa ta the Rally of Republicans, da kuma gwamnatin hadaka da take ciki.

'Yan hamayya ba su shiga zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar shekara biyar da suka wuce ba sakamakon rikicin da ya barke wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3000.

Ana yi wa Laurent Gbagbo, mutumin da Mr Ouattara ya gada, shari'a a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya bisa zarginsa da aikata laifukan cin zarafin bil adama.

Jam'iyyarsa, the Ivorian Popular Front, za ta fafata a zaben na ranar Lahadi.