Harin da aka kai wa kasuwar Kirsimeti a Berlin
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kai harin ne a lokacin da mutane ke hada-hada a birnin Berlin da ke Jamus

Mutane goma sha biyu ne suka rasa rayukansu a lokacin da babbar motar ta afkawa kasuwar.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta bayana harin a matsayin babban laifi.

Merkel ta ce za a yi nazari kan lamarin, kuma za a hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika kamar yadda dokokin kasa suka tanada.