Dole Yahya Jammeh ya sauka daga mulki — ECOWAS

Adama Barrow ya lashe zabe

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya yi amai ya lashe

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO sun yi kira ga shugaban Gambia Yahya Jammeh da ya mika mulki a watan Janairu.

Shuagabannin sun yi kiran ne a karshen taron kungiyar karo na 50, ranar Asabar, a Abuja, babban birnin Najeriya.

A wata sanarwa da aka fitar a karshen taron, shugabannnin sun ce za a iya amfani da karfin tuwo a kan Jammeh idan yaki sauka kamar yadda aka yi wa Laurent Bagbo a Cote D'voire.

Sun kuma yanke shawarar halartar bikin rantsar da sabon shugaban Gambiyar, Adama Barrow, a watan gobe.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne dai za a rantsar da sabon zababben shugaban kasar tare da mika mashi ragamar mulkin Gambia.

Shugabannin na ECOWAS sun kara da cewa za su dauki dukkan matakan da suka dace, domin tabbatar da an yi amfani da sakamakon zaben shugaban kasar.

Har wayau, kungiyar ta nemi goyon bayan Tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya wajen warware rikicin siyasar na Gambia.

A karshen taron an kuma zabi shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, da shugaban Ghana mai barin gado, John Dramani Mahama, a matsayin wadanda za su jagoranci sasanta takaddamar siyasar a Gambia.

A dai ranar daya ga watan Disamba ne aka gudanr da babban zaben Gambia a inda kuma dan takarar jam'iyar adawa, Adama Barrow ya kayar da shugaban kasar, Yahya Jammeh.

Shugaba Jammeh kuma bai yi wata-wata ba ya taya Adama Barrow murnar lashe zaben.

To sai dai kuma mako daya bayan nan sai shugaba Jammeh ya yi ikirarin lashe zaben,a inda ya yi wurgi da sakamakon zaben na farko.