Nigeria: Yadda jihar Ebonyi ta yi 'zarra' a noman shinkafa

  • Abdussalam Ibrahim
  • BBC Hausa, Ebonyi
Noman shinkafa a Nigeria

Matsalar tsadar abinci da ake fama da ita a Najeriya ta sa gwamnatoci da dama sun farka daga mafarkin da suke cewa man fetur zai iya rike su. Tuni wasu jihohi da ma gwamnatin tarayya suka ce sun fara daukar matakan inganta noma domin ciyar da kai da samun kudaden shiga.

Sai dai wata jiha daya tilo da ake ganin ta yi nisa wuirn bunkasa harkar noman shinkafa ita ce Ebonyi, wacce wasu ke ganin za ta iya ciyar da kasar baki daya.

Tun shekaru fiye da 50 da suka gabata garin Abakaliki, babban birnin jihar da a yanzu aka fi sani da jihar Ebonyi, da ke Kudu maso Gabashin kasar.

Wani mataki da jihar ta dauka a baya-bayan nan shi ne na hana shigar da shinkafar kasar waje domin karfafa wa manoman gida gwiwa ba ya ga sauran matakan da ta ke dauka.

Kwamared Sam Igwe, wani mataimaki na musamman ga gwamnan jihar, ya shaida min cewa baya ga illa ga manoman cikin gida shinkafar ta waje na da hadari ga lafiyar jama'a, inda ya yi zargin mutum biyu sun mutu bayan cin shinkafar.

"Muna sa ran wannan mataki zai taimaka wurin bunkasa noman cikin gida," In ji Mista Igwe.

Bayanan bidiyo,

Ebonyi ce ke kan gaba a noman shinkafa a Nigeria

Sai dai jami'in gwamnatin ya ce, ba wai dungurungum aka hana shiga da sayar da shinkafar wajen ba.

"Ba za mu hana shigo da shinkafar ba, idan har tana da ingancin duk da ya kamata, da takardun da suka dace daga hukumar kula da ingancin kayyaki ta Najeriya da shaidar biyan kudin fito, kuma komai yana bisa ka'id, kafin a shigo da ita. Mutum ya iya sayar da shinkafar ta waje.

Casar shinkafa

Ya kara da cewa za a dauki matakan kwacewa da konawa idan aka kama mutane suna sayarwa ba bisa ka'ida ba.

Don ganin wannan mataki na hana ssayar da shinkafar wajen barkatai a jihar ta Ebonyi ya yi tasiri, musamman gwamnatin jihar ta kafa wata hukuma da ke sa ido kan batun.

Ga dubban manoman jihar Ebonyi dai, hana shigo da shinkafar kasar waje da sayar da ita a duk fadin jihar wani zancen ji ne, kuma abin farin ciki.

Domin hakan zai kara masu kwarin gwiwar yin abin da suka kwashe shekaru aru-aru suna gudanarwa a matsayin wata babbar sana'a, wato noman shinkafa.

Daya daga cikin manoman Okotoka Ogbozogwu ya ce yana noma hekta fiketa fiye da 40.

Ya kara da cewa "A hekta 18, na yanki fiye da buhu 300, kuma ina ci gaba da yanka. A shekara dai ina noma hekta fiye da 40 da damina kadai. Ba ma noman shinkafa na rani, saboda rashin kayan aiki," in ji shi.

Sai dai yayin da wasu manoman ke amfani da inji wajen fyade shinkafarsu, wasu kuwa ba su da halin samun injin. Don haka, da hannu suke aiki, kamar yadda na tarar da wani manomi rike da sanda yana fyadin shinkafarsa.

Wani manomi mai suna Luke Udeh, ya ce "Ba wanda ke tallafa mani da hannuna nake aikin shinkafar, don haka a duk tsawon yini guda buhu uku kawai nake iya fyadewa ni kadai. Da kamar da inji ne abin da zan iya yi zai fi haka matuka."

Wannan ne ma ya sa manoma ke neman tallafi, a cewar Mista Ogbozogwu.

Ita dai shinkafar gida ba wai noma ta a fyade ta zama samfarera ne matsalar ba, yadda za a cashe ta, a fidda tsabarta tsaf-tsaf.

Mafi yawan masu aikin casar shinkafa a jihar Ebonyi dai, manoman shinkafar ne, kuma mutane irinsu Osulor Emmanuel, na ganin alfanun matakin gwamnati na hana sayar da shinkafar waje.

"A da muna fama da kamfar masu sayen shinkafarmu ta gida amma yanzu da yake gwamnati ta dakatar da sayar da shinkafar waje, muna jin dadi game da hakan. Kuma a shirye muke mu samar da yalwatacciyar shinkafa daga namu bangaren."

Ba bambancin farashi

A kokarin kara ingancin shinkafar ta gida, gwamnatin jihar Ebonyi ta kakkafa wasu wuraren casar shinkafa irin na zamani har guda hudu a sassan jihar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mutumin da ke kulda wurin casar Mista Ogbonna, ya ce:"Nan ne muke casar shinkafa, mu sanya ta a buhu, kuma a yanzu muna casa fiye da buhu dari biyar a duk rana. Idan ma ana bukata za mu iya cashe fiye da haka."

Jihar Ebonyi dai, ta hau hanyar kai wa ga wani mataki na bunkasa ta fuskar noma da casar shinkafa, a cewar Kwamred Joseph Onunu, manomin shinkafa, kuma shugaban kungiyar masu casar shinkafa ta jihar.

"Yau muna da karfin samar da shinkafa mai yawa, saboda muna da injinan casar shinkafa fiye da 1,500 mallakar jama'a masu zaman kansu.

Kuma a kullum muna samar tan 180, na buhunan casassar shinkafa a cikin sa'o'i hudu. Idan ma muka sami karin masu yi mana ciniki za mu iya kara adadin da muke samarwa".

Sai dai ra'ayin wani magidanci Onyemaechi Nzekwe ya ce akwai sauran aiki a gaban manoman:

"Na gwammace shinkafar waje fiye da ta gida, domin ta wajen tana ba ni duk abin da nake ra'ayi a shinkafa. Ga shi ba ta da tsakuwa, ga kuma dadi idan an dafa".

Bambancin farashin shinkafar gida da ta wajen ba shi da yawa, domin ana sayar da babban buhun shinkafar gida naira 19,000, ita kuma ta wajen naira 21,500."

Bisa ga dukkan alamu, wannan mataki da gwamnatin jihar Ebonyi ta dauka na hana sayar da shinkafar waje a yankinta, sannu a hankali yana samun tagomashi.

Har ma gwamnatin tarayyar Najeriya ta albarkaci abin.

Wannan kam, wani kyakkyawan albishir ne, da ma kuma masu iya magana kan ce, ''Kowa da hannunsa yake tagumi''.