Solomon Dalung ya umarci a binciki hukumar NFF

NFF
Bayanan hoto,

Hukumar NFF ta musanta zargin yin almubazzaranci

Ministan Wasanni na Nigeria Solomon Dalung ya umarci a gudanar da bincike kan yadda Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar NFF, ke kashe kudadenta.

Hakan ya biyo bayan zargin da aka yi cewa an karkatar da kudadden da hukumar kwallon kafa ta Fifa ta bai wa kasar.

Sai dai hukumar ta NFF ta musanta zargin da Mista Dalung ya yi na cewa kimanin dala 802,000 ta yi batan dabo a hukumar.

Wannan lamari ya sa hukumar Fifa dakatar da tallafin sama da dala miliyan guda da take bai wa kasar.

Amma NFF ta nace cewa babu coge a binciken da aka gudanar na farko, a don haka "labarin kanzan-kurege a ka bai wa ministan".

Sai dai Mista Dalung, wanda ke magana a wurin taron karshen shekara na NFF a Lagos, na son ganin an yi sabon bincike domin duba yadda aka kashe kudaden na Fifa.

Rahotanni sun ce "Fifa ta dakatar da bai wa kasar duk wasu kudade na bunkasa tamola saboda rashin fayyace gaskiya kan yadda aka kashe dala $802,000 da ta bayar," in ji Dalung.

Ya kara da cewa wannan ba karamin lamari ba ne wanda ke bukatar kulawar gaggawa domin kaucewa zubarwa da kasar kima, wanda kuma ya sabawa manufofin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ba dai wannan ne karon farko da ake samun sabani tsakanin ministan da hukumar ta NFF ba.

Ko a 'yan kwanakin nan sai da a ka ji kawunansu saboda gazawar da NFF ta yi wurin biyan 'yan wasan Super Falcons kudadensu bayan lashe gasar cin kofin kasashen Afirka ta mata.