Nigeria: Ana zaman dar-dar a Kafanchan

Bayanan sauti

Nigeria: An kafa dokar hana fita a Kafancan

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a garin Kafanchan da ke kudancin jihar, sakamakon wani kazamin rikici da ya kaure a yankin.

Rikicin ya taso ne biyo bayan wata zanga-zangar da ta rikide har ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Rahotanni sun ce matasan yankin wadanda yawanci mabiya addinin Kirista ne suka fito zanga-zanga domin nuna damuwa game da hare-haren da suka ce ana kaddamarwa a yankin.

Al'umar yankin dai sun sha dora alhakin hare-haren a kan Fulani makiyaya Musulmi, abin da Fulanin suka sha musantawa.

Yayin da hukumomi suka ce suna gudanar da bincike kan rikicin wanda yake nema ya gagari kundila.

Rahotanni sun ce jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a garin don tabbatar da zaman lafiya.

Ku saurari karin bayani a rahoton wakilinmu Nura Muhammad Ringim: