Jamus: Ana binciken harin da aka kai a wata kasuwa

Akalla mutane 12 ne suka mutu 5 kuma suka ji mummunan rauni

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Akalla mutum 12 ne suka mutu biyar kuma suka ji munanan raunuka

Hukumomin kasar Jamus suna yin tambayoyi ga direban motar akori-kura da ya afkawa wata kasuwa da ke ci gabannin bukukuwan Kirsimati a birnin Berlin.

Akalla mutum 12 ne suka mutu, da wasu biyar kuma suka ji munanan raunuka.

Wannan lamari ya abku ne a kasuwar dake Breitscheidplatz, kusa da Kurfuerstendamm, a yammacin birnin Berlin a dai dai lokacin da jama'a da ke ta hada-hada yayin da wasu kuma ke shakatawa.

Kasuwar ta shahara wajen sayar da kayayyakin da ake sakawa da hannu, da kayayyakin ka-wa-ta wurare, da sauran kayayyakin wasanni na yara masu ban sha'awa.

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere, ya ce akwai alamun an kai harin ne da gangan.

Wasu rahotannin sun ambato jami'an tsaron Jamus na cewa direban motar wani dan Afghanistan ne ko kuma Pakistan da ya nemi mafaka a kasar.