Arik Air ya dakatar da jigila saboda zanga-zangar ma'aikata

Ma'aikatan na neman biyan su hakkokinsu Hakkin mallakar hoto Arik
Image caption Zanga-zangar ta tilasta dakatar da tashin jiragen Arik

Ma'aikatan kamfanin jiragin sama mafi girma a Najeria Arik, sun gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos.

Masu zanga-zangar sun tilasta rufe ofisoshin kamfanin inda ayyuka suka tsaya cak.

Ma'aikatan dai na zanga-zangar ne bisa zargin kamfanin da kin biyansu hakkokin su na tsawon wata bakwai.

Bayanai daga filayen tashin jiragen sama na Abuja da Kano sun bayyana cewa ayyukan kamfanin na Arik sun tsaya cak a can ma.

Wani fasinja ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ala tilas ya fasa tafiyar da ya shirya yi sakamakon matakin ma'aikatan.

Ya kara da cewa babu wani jami'in kamfanin na Arik da ya ke yi wa fasinjoji-da suka rasa na yi- bayanin hali da ake ciki.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kamfanin na Arik ya bayyana cewa zai rage zirga-zirga ta cikin gida sakamakon karancin man jirgin sama.

Image caption Ma'aikatan sun toshe kofar shiga kamfanin da ke Lagos
Image caption Ma'aikatan na neman a inganta musu yanayin aik, kuma a biya su albashin da suke bi

Labarai masu alaka