Mutum 29 sun mutu a wata kasuwar Mexico

Hotunan kungiyar agaji ta Red Cross sun nuna yadda shaguna suka yi kaca kaca

Asalin hoton, MEXICAN RED CROSS/TWITTER

Bayanan hoto,

Hotunan kungiyar agaji ta Red Cross sun nuna yadda

Wasu abubuwan fashewa sun tashi a kasar Mexico a wata fitacciyar kasuwar sayar da kayan wutar da ake amfani da su a lokacin bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara inda mutum 29 suka rasu.

Wasu da dama kuma sun jikkata yawancin su kuma konewa suka yi.

Kasuwar da ke wajen babban birnin kasar da ke Tultepec makare ta ke da mutane masu siyayyar bukukuwan Kirsimati, a lokacin da ababen suka fashe.

Wakilin BBC ya ce a daidai lokacin da adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ke kara yawa, a bangare guda kuma ana ci gaba da samun karin haske game da wadanda suka jikkata.

Wasu hotunan internet da gidajen talabijin din kasar suka wallafa sun nuna yadda hayaki ya turnuke sama a kasuwar da ke Tultepec.

Mutane dai sun firgita matuka inda suka fara gudun ceton rai, ya yin da wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya.

Tuni hukumomin kasar suka sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifi a fashewar ababuwan da suka sanya mutane cikin rudani.