An saki James Ibori na Nigeria daga kurkuku a Ingila

James Ibori

Asalin hoton, METROPOLITAN POLICE

Bayanan hoto,

An yanke wa James Ibori hukuncin daurin shekara 13 a shekarar 2012 saboda halatta kudaden haram

An saki tsohon gwamnan jihar Delta a Nigeria James Ibori daga gidan Yari a Birtaniya duk kuwa da yunkurin da sakatariyar harkokin cikin gida ta yi na ganin an ci gaba da tsare shi.

A ranar Talata ne ya kamata dama ace an sake shi, bayan ya amince a tasa-keyarsa bayan ya kwashe rabin shekaru 13 da aka yanke masa na zaman gidan yari.

Amma a yanzu ta bayyana cewa Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya Amber Rudd ba ta da niyyar tasa-keyar Iborin zuwa Nigeria har sai ya mika wasu miliyoyin kudade.

Gwamnatin Birtaniya na son ya mika mata fam miliyan 18 daga cikin kudaden da ya samu ta hanyar aikata laifi.

A shekarar 2012 ne aka yanke wa James Ibori hukuncin daurin shekara 13 a gidan yari saboda halatta kudaden haram.

Har yanzu kuma yana da tuhume-tuhume da yake fuskanta a mahaifarsa, Najeriya.

Mista Ibori ya jagoranci jihar Delta ne daga shekarar 1999 zuwa 2007.