Hotunan birnin Aleppo a da da kuma yanzu

Interactive

2016

View from the citadel across the devastated city

2008

View from the Citadel of people eating at restaurants

Aleppo shi ne birni na biyu mafi girma a Syria, kuma a baya shi ne cibiyar masana'antu da hada-hadar kasuwanci, da kuma matattarar masu yawon bude ido.

Amma shekara hudu da aka yi ana fama da yaki, ya bar garin da ke cike da muhimman tarihi - kuma mazaunin Hukumar Unesco - a lalace.

A yayin da aka soma kammala kwashe fararen hula daga yankunan da ke hannun 'yan tawaye a gabashin Aleppo, kuma dakarun gwamnati suka kwace iko da birnin, an soma fidda wasu hotuna da ke nuna yadda garin ya koma.

Tsohuwar fada

Interactive

2016

The entrance to the citadel in December 2016

2010

The entrance to the citadel in August 2010

Gidan tarihin Aleppo a karni na 13 - na daya daga cikin fitattun gine-ginen tarihi a kasar, amma a yanzu yakin ya rugurguza shi ciki da waje.

Dakarun gwamnatin Syria sun yi amfani da tsohon ginin a matsayin garkuwa, inda sakamakon haka ne kuma ya sha hare-hare daga mayakan 'yan tawaye.

Masallacin Umayyad: Ranar 6 ga watan Oktoban 2010, da 17 ga watan Disamba 2016.

Daga bangaren yammacin tsohuwar fadar, akwai babban Masallacin Umayyad - wanda aka gina tsakanin karni na 8 da na 13, kuma a yanzu ya kusa zama kasa baki daya.

An rushe hasumiyar masallacin mai tsawon mita 45, shekaru uku da suka gabata.

Makarantar Al-Shibani

Interactive

2016

The school has been badly damaged during the fighting in Aleppo, pictured December 2016

2009

People attend a music concert in the school courtyard in June 2009

Makarantar Al-Shibani, daga karni na 12 na daga bangaren kudancin masallacin wanda ya zamo matattarar shagulgula na al'ada da baje koli, bayan an sake yi mata gyara.

Yanzu dai an kauracewa cibiyar, wacce ke bukatar gagarumin aiki wajen sake gina ta.

Hammam al-Nahasin: Ranar 6 ga watan Oktoban 2010 da 17 ga watan Disamba 2016.

Asalin hoton, Reuters

Hammam al-Nahasin, wanda ita ma ke bangaren kudu ga masallacin, tana tsakiyar wata tsohuwar kasuwar da za ta kai tun karni na 13 a birnin Aleppo.

Ginin gyaran jikin na maza zalla na daya daga cikin matattarar masu yawon bude ido tun kafin a soma yakin basasar.

Kasuwar Shabha: Ranar 12 ga watan Disamba 2009 da 16 ga watan Octoba 2014

Asalin hoton, Reuters

Ba kuma tsohon birnin ne kawai aka lalata ba. Yakin ya kuma yi sanadin rufe kasuwar Shabha - daya daga cikin manyan kasuwanni inda ake da rukunin kantuna a birnin.

Rahotanni dai sun ce a baya mayakan IS sun yi amfani da ginin jerin kantunan a matsayin wurin ajiye fursunoni, kafin daga bisani kungiyar masu jihadi ta Al-Nusra Front ta kwace iko da shi.

Dukkanin hotunan Reuters ce ta dauke su.