Hotunan kananan dabbobi da kwari wanda aka dauka domin fitar da surarsu

Hoton Kadangaren dajin da Muhammad Roem ya dauka

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Wannan hoton Kadangaren da ke yin gwalo, shi ne hoton da Muhammad Roem ya ce ya fi kauna cikin hotunansa

Akwai hotunan da aka dauka kusa-kusa, akwai kuma wasu da Muhammad Roem ya dauka, wani mai daukar hoto a Indonesiya, wanda bai gama kwarewa ba a aikinsa.

Daga hotunan rawar kwadi, sai hotunan kadangaru, babu dai abun da ya gitta wa Kamarar Mista Roem, mai shekaru 28.

Ma'aikacin jinyar, ya soma aikin daukan hotuna ne shekaru uku da suka wuce, kawai domin sha'awa.

Yanzu kuma mai daukan hoton, wanda mazaunin Batam ne, yana amfani da lokacin da ya samu domin daukan hoton dabbobi a daji.

"Ina bin kwari domin na dauki hoton siffar yadda suke. Wasu lokutan, cikin hotunan dana dauka, da kyar ake samun guda daya kacal da aka samu siffar da kyau. A wasu lokutan ma bana samun komai."

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Wasu hotunan da Muhammad Roem ya dauka sun yi kama da almara

Mista Roem ya ce, "Yawancin mutane basa ganin komai a sassan jikin dabbobi."

Ya kuma kara da cewa, "Ina kokari na fiddo da wani sassa na musamman, misali idan ka kalli idanunsu,- gwanin sha'awa."

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

In har ka kifta idanunka to zaka rasa shi - kamar yadda hoton wannan Kadangaren ya nuna

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Ga alama Roem dai na sha'awar Kwadi

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Ya fi yin amfani da kamara mai kimanin milimita 100, amma ya kan sauya kamarar zuwa MP E mai milimita 65 idan yana bukatar ganin abun da ke nesa

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Fasaha mai ban mamaki, inda hoton ya nuna ja da bakin launin rina

Asalin hoton, Muhammad Roem

Bayanan hoto,

Har kana iya jin digar ruwan sama daga wannan hoton da na kuda

"Na fara koyan daukan hoto ne da kai na, daga baya sai na soma neman shawarar kwararru" In ji Mista Roem. "yawancin lokuta ina zagaye garin Batam ina daukan hotuna, amma idan na samu loakaci sai in kama hanyar tafiya Indonesiya."

Yanayin aikin sa na ma'aikacin jinya, baya ba shi lokaci sosai wajen sha'awarsa ta daukan hoto, amma idan ya samu dama, sai ya dauki mako guda yana gyara hoto daya.

"Ina daukan rana guda domin in dauki hoto daya kacal." In ji shi, "Amma kuma sai na kwashe mako daya ina aikin gayar hoton."

Hotunan da Muhammad Roem ya dauka.