Ana neman dan Tunisia kan harin Berlin

An tsaurara tsaro a Jamus bayan harin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An tsaurara tsaro a Jamus bayan harin

Kafofin watsa labarai sun ce 'yan sandan kasar Jamus na neman wani dan kasar Tunisia saboda zargin kai hari a wata kasuwar Kirsimeto a birnin Berlin.

Rahotanni sun ce wasu takardu da aka gano a cikin motar da ta fada wa taron mutanen sun ce an haifi mutumin, mai suna Anis A, a shekarar 1992 a birnin Tataouine.

'Yan sanda sun soma yin bincike a jihar Arewacin Rhine-Westphalia.

Ana tsammani mutumin da ake zargi ya ji rauni a lokacin da yake kokawa da direban motar.

Jaridun Allgemeine Zeitung da Bild sun ruwaito cewa dan kasar ta Tunisia da ake zargi da kai harin yana da tsakanin shekara 21 zuwa 23 kuma yana yin amfani da sunayen karya.

Jaridar Sueddeutsche Zeitung ta ce ya nemi mafaka a watan Afrilu kuma an ba shi izinin zama a kasar na dan wani lokaci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An saki mutumin da ake zargi