Tsoron kaciya ya hana 'yan mata komawa gida a Kenya

Students walk in a line wearing orange t-shirts that say "Protect girls, say no to FGM" and white t-shirts saying: Run To end FGM

Daruruwan mata 'yan makarantar-kwana a kasar Kenya ne suka ki tafiya gida domin yin hutun Kirsimeti domin fargabar da suke yi cewa iyayensu za su tursasa musu a yi musu kaciya.

Yanzu dai makarantun da suka kamata su rufe domin a tafi hutu na ci gaba da zama a bude saboda 'yan matana sun ki tafiya gida, yayin da wasu 'yan makarantar suka koma kwana a coci-coci a lardin Pokot da ke arewa maso yammacin Kenya.

Alice Jebet, mai shekara 14, ta ce iyayensu za su sa a yi musu kaciya ne domin dalilai na samun kudi da kuma na al'ada.

Ta shaida wa BBC ce,wa "Iyayena na tilasta wa a yi mana kaciya saboda su karbi sadaki mai tsoka.Idan aka yi wa yarinya kaciya, nan da nan iyayenta za su yi mata aure. Kuma da zarar sun gama shirya su, za a tura su dakunan mazajensu, wadanda za su bayar da shanu a matsayin sadaki."

Ana ci gaba da yi wa mata kaciya a kasar Kenya duk da doka mai tsauri ta hana yin hakan da aka kaddamar a shekarar 2011.

An fi yi wa matan kaciya a lokutan hutu na watan Disamba, lokacin da a al'adance ake bai wa maza da mata damar haduwa da juna.

Bayanan hoto,

Iyaye da 'ya'yansu sun yi gangami domin kyamar kaciyar mata

An bai wa shugabannin makarantu umarnin barin mata 'yan makarantar ci gaba da zuwa azuzuwa a gaba dayan ranakun shekara, domin hana wa a yi musu aure suna da kananan shekaru ko kuma tursasawa a yi musu kaciya.

Wasu alkaluma da gwamnatin kasar ta fitar sun nuna cewa ana yi wa mace daya cikin mata biyar 'yan shekara 15 zuwa 49 kaciya.

Hakan babban abin damuwa ne ga kananan mata, wadanda ake tilasta musu yin kaciya.

Bayanan hoto,

Ana yawaita yi wa mata kaciya a Kenya duk da dokar da aka kaddamar ta haramta yin hakan a 2011

Matan da suka gudu daga gidajensu bisa tsoron kaciya na samun taimako daga 'yan kungiyoyin da ke yaki da yi wa mata kaciya.

A kwanankin baya ne aka gudanar da taron wayar da kan jama'a kan illar yi wa mata kaciya a wata makarantar din maza.

Mata da maza 'yan makaranta da iyayensu sun yi gangami domin kyamar yi wa mata kaciya.