An taba sanya ido kan dan Tunisiyan da ya kai hari a Berlin

Anis Amri, mutumin da ake zargi da kai hari a Berlin

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Anis Amri, mutumin da ake zargi da kai hari a Berlin

A duk fadin Turai ana ci gaba da farautar dan asalin Tunisiyan nan da ake zargi da kai hari a birnin Berlin wanda kuma rahotanni ke cewa jami'an tsaro sun taba sanya idanu a kansa kan ko zai kai harin ta'addanci a farkon shekarar nan.

Rahotanni sun ce an sanya idanu kan Anis Amri, mai shekara 24, inda ake zarginsa da yunkurin yin fashin da makami domin ya biya kudin bindigar da zai saya sai dai an daina sanya idanu a kansa saboda ba a samu cikakkiyar shaida ba.

Ya sha daurin shekara hudu a Italiya bayan an kama shi da aikata laifuka kafin ya shiga Jamus.

Harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti ranar Litinin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 12 da jikkata mutum 49.

An bayar da umarnin kama Amri bayan an gano takardun shaidar zamansa a kasar a cikin motar a-kori-kurar da aka kai hari da ita.

Jami'an gwamnatin Jamus sun yi gargadin cewa mai yiwuwa yana dauke da makamai don haka zai kasance mai hadari, suna masu yin tayin bayar da tukwuicin €100,000 (£84,000; $104,000) ga duk wanda ya bayar da labarin yadda za a kama shi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gana da jami'an tsaron kasar domin tataunawa kan yadda za a fuskancin matsalar tsaron da ta taso sakamakon harin.

A wani bagaren kuma, gwamnatin kasar ta bayar da umarni a sanya na'urorin bidiyo da za su rika sanya ido domin tabbatar da tsaro a kasar.