An yi jana'izar jakadan Rasha da aka kashe a Turkiya

Mr Putin na cikin mutanen da suka sanya fure a kan kawatin gawar Karlov Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Putin na cikin mutanen da suka sanya fure a kan kawatin gawar Karlov

Ana yin jana'izar jakadan Rasha wanda aka harbe har lahira a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.

A ranar Talata ne aka kai gawar Mr Andrei Karlov, wanda wani dan sanda Mevlut Mert Altintas birnin Moscow domin yi masa jana'iza.

Shugaba Vladimir Putin zai yi jawabi a wajen jana'izar da ke ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Bayan ya harbe jakadan, Mr Altintas ya rika ihu yana cewa ya dauki matakin ne a matsayin ramuwar-gayya kan shigar kasar Rasha cikin hare-haren da ake kai wa a Aleppo na Syria.

Ana fargabar cewa kisan jakadan na Rasha a Turkiyya zai sa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, kodayake wakiliyar BBC a Moscow Sarah Rainsford ta ce kasashen sun jaddada abokantakar da ke tsakaninsu.

Rasha da Turkiyya na aiki tare a kan binciken kisan da ake yi.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andrei Karlov yana yin jawabi ranar Litinin ba tare da sanin cewa mutumin da ke bayansa ne zai kashe shi ba

Karlov, mai shekara 62, fitaccen ma'aikacin dipilomasiyya ne wanda ya yi aiki a kasashe da dama ciki har da jakadan Tsohuwar Tarayyar Sobiyat a Koriya ta Arewa a shekarun 1980.

Labarai masu alaka