'Yawan amfani da shafukan zumunta yana sanya ƙyashi'

social media

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

Yawan amfani da shafukan zumunta na sanya damuwa

Wani bincike ya nuna cewa yawan amfani da Facebook a lokacin Kirsimeti da kallon hotunan iyalin da ke da wadata a wuraren shakatawa zai sanya wa mutum kyashi maimakon farin ciki.

Binciken da Jami'ar Copenhagen ta gudanar ya nuna cewa amfani da shafukan zumunta fiye da kima ka iya sanya kyashi a zukatan mutane.

Ya yi gargadin cewa masu yawan amfani da shafukan za su daukar miyagun halaye.

Binciken ya bayar da shawarar cewa ya kamata masu amfani da shafukan su dauki hutun amfani da su.

Binciken ya yi nazari kan mutum 1,300, yawancin su mata, wadanda suka ce "yawan amfani da shafukan sada zumunta musamman Facebook zai iya yin mummunan tasiri a rayuwarsu sannan su rika jin cewa ba su gamsu da baiwar da Allah ya yi musu ba".