Mace ta farko da ta gina asibitin haihuwa a Somaliland

Edna Adan Isma'il ta gina asibitin ne ta hanyar tara kudi da kuma kadarorin da ta mallaka domin rage mutuwar mata a lokacin haihuwa.

Mata da dama na mutuwa a lokacin haihuwa sakamakon rashin kwararrun likitoci ko kuma asibitoci a nahiyar Afirka.