Yaran Syria da ke cikin kunci jarumai ne — Ronaldo

Syrian Children
Bayanan hoto,

Yadda yakan Syria ke fama da karar harbin bindiga ga tashin bama-bamai

Cristiano Ronaldo gwarzon dan kwallon kafa da ya fi yin fice a duniya wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana ya ce yaran Syria da suka dade suna shan bakar wahala jaruman gaske ne.

Dan wasan na Real Madrid ya fadi hakan ne bayan da ya shiga kamfe din samar masu da abinci da magunguna da taimaka wa yaran Aleppo da wadanda yaki ya shafa.

Ronaldo a wani faifan bidiyo da ya fitar a kafar sada zumunta ya ce "Mun san da cewar kuna shan bakar wahala. Ni fitacen dan wasa ne a duniya, amma ku jaruman gaske ne".

Dan kwallon tawagar Portugal ya kara da cewa "Kar ku yanke-kauna ko fidda rai, duniya tana tare da ku, nima ina tare da ku."

Nick Finney na save the children masu yin kamfe don Syria ya ce "Ronaldo ba wai kawai daya ne daga cikin fitattu a fagen wasa ba ne, ya kuma zama tsani na fatan da miliyoyin yara maza da mata ke son zama a fadin duniya."

A kalla yara 15,000 na daga cikin sama da mutane 300,000 da aka kashe a lokacin yakin Syria da aka yi tsawon shekara biyar in ji kungiyar da ke taimaka wa kananan yara ta duniya.