Allardyce na kan gaba cikin masu son maye gurbin Pardew a Crystal Palace

Sam Allardyce

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Allardyce ya gudu ya bar ladansa a Ingila

Tsohon kocin Ingila Sam Allardyce na kan gaba cikin masu neman maye gurbin Alan Pardew kocin da Crystal Palace ta kora ranar Alhamis.

Ansallami Pardew saboda rashin katabus din kungiyar a gasar Premier ta Ingila inda take a mataki na 17 bayan da ta ci wasa daya kacal cikin wasanni 11 da ta buga.

A halin da ake ciki Palace dai bata kulla wata yarjejeniya ko kwantaragi Allardyce ba don haka wasu ma za su iya neman wannan mukami.

Sai dai ana sa ran tsohon kocin, mai shekara 62 ne zai samu mukamin bayan da shugaban kungiyar kwallon kafar Steve Parish ya ce salon Pardew na wasa bai yi amfani ba.

Parish ya shaida wa BBC cewa "Yanzu za mu nemi wanda zai sauya tsarin buga wasa."

Allardyce ba shi da aiki tun da aka kore shi daga kocin Ingila bayan ya yi kwana 67 a kan mukamin.