Labaran Afirka na 2016 da watakila suka wuce ku

Composite image from photos below

Afirka ta bayar da tata gudunmuwar wajen aikin jarida a bana, amma kuma duk da jaridu sun mamaye nahiyar da labaran gudun hijira da kisan kiyashi, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta zabo wasu labaran masu kayatarwa da watakila suka wuce ku.

Sumbata mafi dadewa

Asalin hoton, AP

Ga dan Majalisar Zimbabwe Joseph Chinotimba, mai goyon bayan shugaban kasar Robert Magabe, ya fara shekarar 2016 da soyayya.

Dan Majalisar mai shekaru 66, kuma tsohon sojan ya sumbaci matarsa Vimbai, a yayin wata gasa ta ranar masoya watau Valentine, inda suka yi nasarar lashe gasar.

Ma'auratan da suka shekara takwas da aure sun lashe kyautar wadanda suka fi kowa dadewa suna sumbatar juna , inda suka kai minti 10 da dakikoki 17 suna sumbatar juna, hakan kuma ya sanya suka doke ma'auratan bara da minti biyar da dakikoki 17.

Amma duk da haka dai soyayyar Chinotimban, ba su kamo kafar ta wasu ma'aurata a Thailand ba, wadanda suka jera sa'ao'i 58 da mintuna 35 da dakikoki 58 suna sumbatar juna.

Siyasar daidaita sahu

A cikin shekarar kuma, an samu wani dan Majalisar Najeriya da ya bayar da misalin yadda har yanzu mata ke da sauran aiki wajen yaki da masu cin zarafin su, da rashin samun daidato a kasar.

Asalin hoton, Oluremi Tinubu

Bayanan hoto,

Oluremi Tinubu ta zamo Sanata a shekarar 2011

Bayan wani kace-na-ce da aka yi cikin sirri a Majalisar Dattijai a watan Yuli, an zargi Dino Melaye da yin barzanar duka da kuma yi wa wata abokiyar aikinsa Oluremi Tinubu ciki.

Mista Melaye dai ya musanata aikata hakan, inda a wata sanarwa da ya fitar ta ban mamaki ya kare kansa da cewa, "Ai babu yadda za a yi in yi mata ciki domin yanzu ai ta tsufa."

Jaridar Punch ta Najeriya ta ambato Misis Tinubu na cewa, ita ta yafe masa kalaman nasa, amma ba za ta bari a cima mata fuska ba a kasar da har yanzu ke da akidar mazan jiya.

Duk da hanyoyi daban-daban da ake bi wajen take hakkin mata a Afirka, suna da damar yin zabe.

Masu zabe da jan farce

Asalin hoton, Thinkstock

Amma kuma a yayin zaben Zambia, ba a bar mata da ke sanye da jan farce sun yi zabe ba, sai bayan sun goge shi tsaf.

Jami'an gudanar da zaben dai sun yi korafin cewa jan farcen ba ya bari su sanya masu tawadar tantance wadanda suka kada kuri'a da kyau ba.

Lamarin dai ya sauya a watan Agusta, inda Zambia ta gudanar da zaben da ya bai wa Edgar Lungu damar wani wa'adin mulkin, kuma kwanaki kadan kafin zaben shugaban hukumar zaben kasar ta fitar da sanarwa ta shafin sada zumunta kan cewa an hana mata da suka sanya jan farce da damar yin zabe.

Maza za su fuskanci gidan kaso bisa aikata laifin zina

Asalin hoton, Thinkstock

A wani yunkurin daidaita sahu tsakanin maza da mata kuma na ban mamaki, a watan Yuni ne Majalisar Kamaru ta yi muhawara kan wata sabuwar doka da za ta tabbatar duk namijin da ya aikata zina, an kulle shi a gidan kaso.

Dama can matan Kamaru na fuskantar watanni shida a gidan kaso bisa laifin aikata zina da aurensu.

An amince da sabuwar dokar, wacce ta samu goyon bayan jami'iyyar Shugaba Paul Biya, inda yanzu mazan kasar ke fuskantar shekara shida a gidan maza bisa laifin aikata zina, ko kuma su biya tarar dala 160.

'Yaro kyakkyawa' da harsashin bindiga

Asalin hoton, Aware Trust Zimbabwe

Zakin nan Cecil ya bar duniya, kuma akwai yiwuwar wasu cikin mu sun manta da shi, amma wani namijin Giwa a Zimbabwe ya ki bari masu farauta su yi sanadin tafiyarsa lahira.

An masa lakabi da 'Pretty Boy' watau 'Kyakkyawan yaro', ya kuma kwashe makwannin uku zuwa shida da harsashin bindiga a goshin sa, kafin likitocin dabbobi na Mana Pools National Park, suka sama masa lafiya a watan Yuni.

An haramta yawan surutu a Legas

Asalin hoton, AFP

Ba zai zo maka da mamaki ba idan ka tarar da taron jama'a da ke hira cikin raha da kakkarfar murya a filayen saukar jiragen sama na kasa-da-kasa, 'yan Najeriya ne.

Ko da a cikin hira ne ko taron walima ko wani biki, 'yan kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka ne za ka tarar cikin annashuwa da kakkarfar murya.

Amma a watan Yuni hukumomi a Legas suka yanke shawarar kawo karshen hayaniyar da ake yi ta wakokin Kiristoci da na kiran sallar Musulmi, inda suka rufe Coci-coci 70, da Masallatai 20 da aka zarga da yawan damun jama'a a jihar.

Cire adiko a shirin talabijan

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Nontobeko Sibisi ta samu goyon baya matuka a shafukan sada zumunta

Mata a Afirka ta Kudu dai kamar sun fi mayar da hankali wajen gudanar da zanga-zanga kan abin da za su sanya ga kawunansu.

Baya ga zanga-zangar da suka sha yi kan wanne irin kitso ya kamata su yi a makaranta, akwai kuma wacce aka yi a kan 'doek', watau adiko a wurin aiki.

Hakan ya biyo bayan samun labarin cewa an katse wata 'yar jaridar tashar ENCA ta kasar, a yayin da ta ke watsa labarai, a dalilin sanya doek din da ta yi.

Bayan cece-ku-cen da lamarin ya janyo, kafar yada labaran ta fito ta ce ka'idar aikin ta bai bari mata su rufe kawunan su ba, amma za ta sake duba ka'idojin nata, domin tashar ba ta amince da wariyar launin fata ba.

Sanya hijabi a makarantu

Asalin hoton, AFP

Amma kuma ga masu sanya hijabi, bana ta yi masu kyau, ganin yadda aka yi ta haramta sanya hijabin a wasu nahiyoyin a shekarar 2015.

Kotuna daban-daban a kasashen Kenya da Najeriya ne suka yanke hukuncin cewa ba za a haramtawa matan sanya hijabi a makaranta ba, ko da kuwa a makarantun Kiristoci ne.

Lamarin dai ya janyo yakin kayayyakin addini a jihar Osun, inda dalibai mabiya addinin Kirista suka sanya dogayen kayan su na coci a saman rigar makarantar su, zuwa makaranta.

Kyawun Zabiya

Kenya kuma ta kammala shekarar da gasar sarakunan kyau tsakanin zabiya a kasar.

Jairus Ong'etta ne ya lashe kyautar Mista Albinism, watau Zabiyan da ya yi fice, inda rahotanni suka ambato shi yana cewa, "Zan tabbata a kan al'adar rubutu da farin alli kan bakin allo, da kuma bakar tawada kan farar takaradar Baybul."

Ya kara da cewa, "Saboda haka launin fari a Kenya ba wai zaman lafiya ya ke nufi kadai ba, yana nufin mutane da kuma fuskokin mutane."