An kashe Anis Amri, mutumin da ya kai hari a Berlin

Asalin hoton, BKA / HANDOUT
'Yan sandan Jamus sun fitar da hotunan Anis Amri
Ministan cikin gida na Italiya ya ce an harbe har lahira Anas Amri, mutumin da ake zargi da kai hari a wata kasuwar Kirsimeti da ke Berlin na kasar Jamus.
Ministan Marco Minetti ya ce Amri ya bude wuta kan 'yan sandan da ke sintiri bayan sun bukaci ya nuna musu katin shaidarsa a yankin Sesto San Giovanni da safiyar ranar Juma'a, yana mai cewa "babu shakka mutumin da aka harbe Anis Amri ne."
An jikkata dan sanda daya a musayar wutan da aka yi.
Jamsu ta tsaurara matakan tsaro tun bayan harin da ya kai wanda ya kashe mutum 12 tare da jikkata mutum 49.
Kafofin watsa labaran Italiya sun rawaito cewa hoton yatsun da aka gwada ya nuna cewa na dan kasar ta Tunisia.
A wani gefen kuma, 'yan sanda sun kama mutum biyu a birnin Oberhausen na kasar Jamus saboda zarginsu yunkurin kitsa kai hari.