Kun ga hotunan Afirka masu kyawu na wannan makon?
Wasu daga cikin hotunan da aka dauka a Afirka a wannan makon:

Asalin hoton, AFP
Mutum biyu sun yi shiga irin ta kayan ninkaya na Santa Claus a wajen wata gasa kan iya ruwa a birnin Durban na Afirka ta Kudu
Asalin hoton, AFP
Haka kuma wannan mutumin da ya yi shiga irin ta Santa ya tsaya kusa da mai dakin shugaban Ivory Coast's first lady Dominique Ouattara (wacce ke tsakiya) da kuma kananan yara a fadar shugaban kasar da ke Abidjan a yayin da ake shirye-shiryen bikin Kirsimeti.
Asalin hoton, AFP
Wadannan mutanen biyu da ke bayan a-kori-kurar da ke dauke da kayan-miya a birnin Lagos na Najeriya
Asalin hoton, AFP
Wasu masunta a Somali na fito da kifin da suka kama daga kwale-kwale a gabar tekun Bosaso da ke yankin Puntland na arewa maso gabashin kasar.
Asalin hoton, EPA
Wannan mutumin na yunkurin tsallake wannan katon ramin a yankin Highfields na Harare, babban birnin kasar Zimbabwe
Asalin hoton, AFP
Shi kuwa wannan mutumin da ke gwada kwanjinsa yana kallon kansa a madubi bayan ya gama motsa jiki a Kampala, babban birnin Uganda...
Asalin hoton, AFP
Shi ma wannan mutumin yana wurin motsa jikin da wancan yake a lokacin
Asalin hoton, AFP
Matasa na wasan kwallon kafa a birnin Sirte na kasar Libya bayan an kori mayakan kungiyar IS daga birnin.
Asalin hoton, AFP
Wannan mutumin kuwa ya dauki hoton dauki-kanka tare da rakumin dawa a gidan ajiye rakuman dawa na Nairobi ranar Laraba
Asalin hoton, Reuters
Ma'aska na yi wa masu hulda da su aski a lardin Lingwala da ke Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimkoradiyyar Kongo.
Asalin hoton, AFP
A ranar Tatala, wadannan sojojin na Burkina Faso sun rike hotunan takwarorinsu 12 da kungiyar IS ta kashe a bakin-aiki kwanaki kadan da suka wuce.
Asalin hoton, EPA
Sojojin da ke faretin ban-girma sun tsaya kyam a filin jirgin saman Abuja na Najeriya a lokacin da Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ke wucewa.
Asalin hoton, EPA
'Yan kasar Tunisia na zanga-zanga bayan kisan wani injiniyan jiragen sama Mohamed Zouari, a dandalin Habib Bourgiba da ke Tunis, babban birnin kasar.
An samu hotunan ne daga AFP, EPA, da kuma Reuters