Dakarun senegal na shirin ko-ta-kwana don kawar da Jammeh

An zabi Senegal domin jagorantar dakarun da za su kawar da Jammeh daga mulki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An zabi Senegal domin jagorantar dakarun da za su kawar da Jammeh daga mulki

Kungiyar Ecowas ta ce an sanya dakarun kasar Senegal a cikin shirin ko-ta-kwana domin tunbuke Shugaba Yahya Jammeh daga kan mulkin Gambia idan ya ki sauka bayan wa'adinsa ya cika.

Tun da farko dai Mr Jammeh ya amince da shan kaye a zaben da aka yi ranar daya ga watan Disamba, amma daga bisani ya ce ba zai sauka ba saboda an yi wasu kura kurai a zaben.

Shugaban Ecowas ya ce an zabi kasar Senegal domin ta jagoranci shirin "dawowa da 'yan kasar Gambia martabarsu" idan bukatar hakan ta taso.

Tuni dai Shugaba Jammeh ya ce babu wanda ya iya ya yi masa barazana domin ya sauka, yana mai cewa Ecowas ba ta da hurumin cire shi daga mulki.

Mr Jammeh, mutumin da ya kwashe shekara 22 a kan mulki, ya shigaer da kara a kotun kolin kasar domin ta soke zaben bayan hukumar zaben ta sauya wasu sakamakon zaben.

Hukumar ta dage cewa sauye-sauyen da ta yi wa sakamakon zaben ba zai sauya yawan kuri'un da suka bai wa Adama Barrow nasara ba don haka ya kamata a rantsar da shi ranar 19 ga watan Janairu.