Ibori: Yadda 'ɓarawo' ya kusa zama shugaban Najeriya

James Ibori (file photo)

Asalin hoton, AFP

Labarin James Ibori, mutumin da aka samu da laifin sata a Birtaniya a shekarun 1990 sannan ya zama gwamnan jiha mai arzikin man fetur a Najeriya kuma daga bisani aka daure shi, batu ne mai cike da al'ajabi.

Shi dan siyasa ne mai matukar wayo wanda ke goyon bayan mutumin da yake gani zai lashe zabe, sannan ya sauya sheka da zarar ya ga hanya ba za ta bulle ba.

Wani mai sharhi ya ce ba don an samu akasi ba da James Ibori ya zama shugaban kasar Najeriya maimakon shan dauri a gidan-yarin Birtaniya.

A koda yaushe aka bijiro masa da zarge-zargen cin hanci da satar kudin jiharsa yakan ce shi fitaccen dan kasuwa ne, wanda ya samu makudan kudi kafin ya shiga harkokin siyasa.

A shekarar 1991 ya yi aiki a wani kanti da ke unguwar Neasden ta birnin London.

Mai shigar da kara a shari'ar da aka yi wa Mr Ibori ya ce albashin Iborin bai wuce £15,000 ba a shekara.

Masu kantin da Mr Ibori ya yi aiki sun kama shi da laifin barin matarsa ta rika dibar kayan kantin ba tare da ta biya kudinsu ba.

Sun amsa laifinsu a kotun Isleworth Crown da ke London kuma an ci su tara.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto,

Ibori ya rubuta sunan kanwarsa da mai yi masa aiki a jikin wasu kadarorin da ya mallaka ta hanyar sata domin ya bad-da-sawu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

'Cuwa-cuwa'

A shekarar 1992, an sami Mr Ibori da laifin mallakar katin cirar kudi na sata, wanda a lokacin tuni ya kashe £1,000 kuma kotu ta kara cin tararsa a kan wannan laifi.

Daga nan ne Ibori ya koma Najeriya da niyyar shiga harkokin siyasa. A lokacin ana shirin komawa turbar dimokradiyya daga mulkin soji.

Shugaban gwamnatin mulkin soji na wancan lokacin Ibrahim Babangida ya shirya gudanar da zabe domin kasar ta koma dimokradiyya a watan Yunin shekarar 1993.

Ibori ya yi wa wani abokinsa da ke son yin takarar gwamna yakin neman zabe.

Kuma rawar da ya taka a lokacin ta sa ya yi hulda da mutane daban-daban, lamarin da ya sa bai sha wata wahala sosai ba lokacin da aka kafa jam'iyyar People's Democratic Party, PDP wacce ta mulki Najeriya tsawon shekara 16.

Janar Babangida dai ya soke zaben shekarar 1993. Bayan ya kwace mulki daga gwamnatin rikon-kwarya ne Janar Sani Abacha ya ci gaba da yin mulki na shekara biyar.

Wani dan jarida da ya kwashe shekara da shekaru yana aiki a Najeriya, Antony Goldman, wanda kuma ya bibiyi harkokin siyasar Ibori sosai, ya ce a lokacin ne Ibori ya fara taka rawa a harkokin siyasa inda ya nemi ya yi aiki da gwamnatin Abacha.

Mr Goldman ya ce "Ba a fayyace takamaimai rawar da ya taka a fannin tsaro ba. Zai iya taka kowacce rawa domin harkokin Najeriya a murde suke."

A tsakiyar shekarun 1990, hukumar binciken laifuka ta Amurka, FBI ta yi wa Ibori tambayoyi a Amurka kan yadda ya samu miliyoyin dalar da ya sanya a wasu asussa na kasar.

FBI ta yi zargin cewa ya samu kudin ne ta hanyar zamba-cikin-aminci, sai dai ya nuna mata cewa ya samu kudin ne ta hanyar harkokin tsaro na gwamnatin Abacha, a cewar Mr Goldman.

Bayan Abacha ya mutu a shekarar 1998 Ibori ya zama babban abokin tafiyar fitaccen dan siyasar nan Atiku Abubakar, wanda ya zama mataimakin shugaban kasa.

'Ya shirga karya kan ranar haihuwarsa'

A shekarar 1999, Ibori ya sayi wani gida a kan titin Abbey Road da ke birnin London da zummar biyan kudin kadan-kadan.

Ya yi hakan ne ta hanyar mallakar sabon fasfo wanda ya nuna sabuwar ranar haihuwarsa domin ya guje wa yiwuwar hana shi mallakar gidan tunda an taba kama shi da laifi a Birtaniya.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

James Ibori ya sha dauri a Birtaniya

Sai dai bai yi katari ba domin kuwa sabuwar ranar haihuwar tasa ta zo daidai da wata daya bayan haihuwar kanwarsa, lamarin da ba zai taba yiwuwa ba, a cewar masu shigar da kara.

An zabi Ibori a matsayin gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur a shekarar 1999.

Ya sha rantsuwar cewa bai taba aikata lafi ba.

Har yanzu da sabuwar ranar haihuwarsa yake amfani.

Ibori ya kammala biyan kudin gidan da ya saya a London jim kadan bayan ya zama gwamna.

Ya kara sayen gidaje uku a Birtaniya. Ibori ya biya £2.2m lakadan wajen sayen wani gida da ke yankin Hampstead na birnin London.

'Shi ne ya dauki nauyin zaben Yar'Adua'

A shekarar 2005 rundunar 'yan sandan birnin London ta soma sanya ido a kan Ibori bayan ya je sayen wani jirgi mai saukar-ungulu ta hanyar wani lauyansa da ke London.

Bayan haka ne Ibori ya tsaya tsayin-daka domin ganin Atiku Abubakar ya maye gurbin Shugaba Olusegun Obasanjo.

A shekarar 2006, Obasanjo ya bukaci James Ibori ya shige gaba domin tabbatar da ganin an sauya kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai samu damar yin ta-zarce.

Bayan wannan yunkuri bai yi nasara ba ne sai Ibori ya yi alkawarin goyi bayan mutumin da zai gaji Obasanjo, wato Umaru Yar'Adua a zaben da ke tafe.

Shi ne ya daga hannun 'Yar Adua a wajen babban taron fitar da gwani na jam'iyyar PDP a shekarar 2006 domin ya nuna cewa su ne da nasara - sa'o'i kadan kafin ma a yi zaben fitar da gwanin.

An zargi Ibori da daukar nauyin takarar Yar'Adua a zaben 2007, kodayake ya musanta.

Mr Goldman ya ce ya fahimci cewa an yi wa Ibori tayin ba shi mukamin mataimakin shugaban kasa saboda rawar da ya taka wajen tsayar da 'Yar Adua.

Sai dai hakan bai yiwu ba kuma 'Yar'Adua, wanda ya rika fuskantar matsalar rashin lafiya, ya mutu yana kan mulki.

Mataimakinsa Goodluck Jonathan ne ya gaje shi.

Duk da yake Ibori tsohon gwamnan jihar Delta da ke yankin Naija Delta ne amma ba sa ga-maciji tsakaninsa da Jonathan.

A shekarar 2010, Jonathan ya sa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta kama Ibori, sai dai magoya bayansa sun yi wa jami'an hukumar kwanton-bauna lokacin da suka je kama shi.

Bayan haka ne Ibori ya fice daga Najeriya.

Ya shiga birnin Dubai, inda gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta kama shi sannan ta mika shi ga Birtaniya domin a yi masa shari'a, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 13.

A wannan makon ne aka saki tsohon gwamnan na jihar Delta daga gidan-yarin Birtaniya domin ya je Najeriya ya kammala wa'adin zaman gidan-kaso.

Amma zai ci gaba da zama a Birtaniya har sai ya mika £18m daga cikin kudaden da ya samu ta hanyar aikata laifi.

Mr Goldman ya ce da a ce 'Yar'Adua bai mutu ba, kuma ya nada Ibori a matsayin mataimakinsa da ya samu damar zama shugaban Najeriya.