Yadda jami'an gwamnatin Nigeria ke ce-ce-ku-ce kan 'shinkafar roba'

shinkafar roba
Bayanan hoto,

Shinkafar tana rike baki kamar cingam kuma ba ta da dadin kamshi.

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta musanta ikirarin da ministan lafiyar kasar ya yi cewa ta tabbatar da sahihancin 'shinkafar robar' da aka shigar kasar.

Wani babban jami'in hukumar ya ce sakon da ministan ya aike ta sahfinsa na Twitter cewa shinkafar ba ta da illa ba shi ne matsayin hukumar ba.

Minista Isaac Adewole ya bayyana a sakon cewa gwaje-gwajen da NAFDAC ta yi a kan shinkafar ba su gano wata alama da ke nuna cewa ta roba ce ba.

Hukumar fara-kwaurin kasar ce dai ta ce ta kwace tan biyu da rabi na 'shinkafar roba'.

'Yan kasar dai na matukar cin shinkafa kuma ya zama wata al'ada sayen shinkafa da yawa a lokutan Kirsimeti.

Shugaban hukumar fara-kwaurin reshen jihar Legas Haruna Mamudu ya shaida wa BBC ranar Laraba cewa an shiga da shinkafar kasar ce da zummar sayarwa a lokacin bukukuwan Kirsimeti, kodayake bai ce komai kan ikirarin da ministan ya yi ba.

Babban jami'in NAFDAC ya shaida wa wakiliyar BBC Stephanie Hegarty cewa har yanzu ana gudanar da gwaje-gwaje kan shinkafar.

A cewarsa, "Ba mu kammala gwaje-gwaje kan shinkafar ba. Za mu kammala nan da kwanaki biyu."

Mr Adewole yace hukumar za ta fitar da "sakamakon cikakken binciken ga 'yan kasar da zarar ta kammala binciken", yana mai yin kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu.

Babu masaniya kan takamaimai inda aka samu shinkafar buhu 102 da aka kwace, amma an samu shinkfar roba a kasar China a shekarar da ta wuce.

Bayanan hoto,

Kowanne buhu yana da nauyin kilogiram 25.

Mr Mamudu ya ce shinkafar tana da tauri baya an dafa ta, yana mai cewa "Allah ne kadai ya san abin da zai faru" da a ce mutane sun ci ta.

Wakilin BBC a Legas Martin Patience, wanda ya taba shinkafar, ya ce ta yi kama da shinkafa ta gaske ama tana kanshin fenti.

Shugaban hukumar fasa-kwaurin reshen jihar Legas ya yi kira a hukunta masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa wadanda ke amfani da lokutan bukukuwa wajen shigo da abubuwan da ka iya cutar da jama'a.

Har yanzu ana sayar da shinkafar a kasuwa?

Ba mu samu wani rahoto da ke nuna cewa ana sayar da shinkafar a kasuwa ba. Jami'an hukumar fasa-kwauri na ci gaba da bincike kan hakan kodayake har yanzu ba su ga masu sayar da ita ba.

Jami'an hukumar fasa-kwaurin sun ce sun kama buhu 102, kuma kowanne buhu yana da nauyin kilogiram 25.

Sai dai babu tabbas kan ko buhu nawa aka sayar.

Akwai wanda ya ci shinkafar?

Babu wani labari kan wani da ya ci shinkafar.

Jami'an hukumar fasa-kwauri sun dafa ta inda suka ce tana rike baki kamar cingam kuma ba ta da dadin kamshi.

A lokacin da aka tambayi Minista Isaac Adewole a Twitter kan ko zai ci shinkafar ya yi barkwanci, inda ya ce ba zai ci ta ba tare da gishiri ba.

'Yan Najeriya sun damu

'Yan Najeriya sun damu matuka da jin labarin shigar da 'shinkafar robar'.

Kafafen watsa labarai sun bayar da rahotanni kan gargadin da ake yi wa 'yan kasar na kada su kuskura su ci duk wani abincin jabu da ake zargi an shigar da shi daga China saboda hatsarin da ke tattare da shi.