Myanmar: An kashe Musulmin da ya yi hira da 'yan jarida

Soji sun kashe Musulmin Rohingya akalla 86 sannan aka tilasta wa fiye da 27,000 f suka tsere daga jihar Rakhine

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Soji sun kashe Musulmin Rohingya akalla 86 sannan aka tilasta wa fiye da 27,000 f suka tsere daga jihar Rakhine

Jami'ai sun ce an gano gawar wani Musulmi dan kabilar Rohingya da aka fille wa kai kwanaki kadan bayan ya shaida wa 'yan jarida irin gallazawar da gwamnatin Myanmar ke yi wa Musulmi a jihar Rakhine.

An gano gawar mutumin mai shekara 41 tana yawa a saman wani kogi ranar Juma'a.

A ranar Laraba ne 'yan uwansa suka nuna fargabarsu bayan ya yi hira da 'yan jaridar kasar, inda ya gaya musu irin cin zarafin da jami'an tsaro ke yi musu.

'Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike game da kisan nasa.

An rufe yankinsu fiye da wata biyu tun bayan wasu masu tayar da kayar baya sun kai hari kan jami'an tsaro da ke aiki a kan iyaka.

BBC ta fahimci cewa mutumin ya shaida wa 'yan jaridar da ba kasafai suke kai ziyara yankin ba cewa sojoji na musguna musu tare da taimakon 'yan kato-da-gora.

A jihar ta Rakhine Musulmi 'yan kabilar Rohingya marasa rinjaye suka fi yawa.

Kungiyar kare hakkin dan adam Amnesty International ta zargi jami'an tsaron kasar da laifin fyade da kisa da kuma gallazawa Musulmin 'yan kabilar Rohingya.

Sai dai jami'an tsaron sun musanta zargin, suna masu cewa kokari suke yi su murkushe 'yan ta'adda.