Jirgin Rasha ya yi hatsari a cikin tekun kusa da Sochi

Jiragen saman Rasha samfurin Tu-154 na yawaita zuwa Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jiragen saman Rasha samfurin Tu-154 na yawaita zuwa Syria

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce wani jirgin sojin kasar dauke da mutum 92 wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Syria daga Sochi ya fada tekun Black Sea.

Na'urar da ke sanya ido kan tafiyar jirgin ta daina jin duriyarsa ne minti 20 bayan ya tashi daga Sochi da misalin karfe 05:20 na safe a agogon kasar. An gano wasu sassan jirgin.

Ma'aikatar tsaron ta ce jirgin, samfurin Tu-154 na dauke ne da sojoji da kuma 'yan jarida.

Jirgin dai ya kan hanyarsa ta zuwa yankin Latakia na kasar Syria.

Jirgin ya taso daga birnin Moscow sanna ya sauka a filin jirgin saman Adler da ke Sochi domin ya kara mai.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron ta Rasha ta fitar ta ce, "An gano wasu sassan jirgin samfurin Tu-154 a nisan kilomita da rabi daga tekun Black Sea da ke kuryar Sochi."

Masu aikin ceto sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Interfax cewa dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun mutu.