Kirsimeti: Mura ta hana Sarauniyar Ingila zuwa Coci

Sarauniyar Ingila a lokacin da take fita daga gidan Sandringham a shekarar 2015

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sarauniyar Ingila a lokacin da take fita daga gidan Sandringham a shekarar 2015

Sarauniyar Ingila ba za ta je coci ranar Kirsimeti domin yin addu'oin da aka saba yi duk shekara ba saboda tana fama da mura, in ji fadar Buckingham.

Tuni mutane suka yi dandazo a katon gidan Sandringham inda suke sa ran ganin Sarauniyar idan ta je cocin.

Sarauniyar da Yarima Philip sun jinkirta soma hutun bukukuwan Kirsimeti da kwana guda, sannan suka soke tafiyar da za su yi saboda murar da ke damunsu.

Ana sa ran sauran 'yan gidan sarautar Birtaniya za su halarci addu'o'in da za a yi a cocin.