'Yadda injin ATM ya hana ni yin bikin kirsimeti'

  • Abdulsalam Usman
  • BBC Abuja
Bayanan bidiyo,

Peter Joseph ya fusata kan ATM

Peter Joseph, dan jihar Nassarawa ne amma yana aiki a Abuja, babban birnin Najeriya.

Peter ya so yin bulaguro zuwa garinsa a jihar Nassarawar domin yin bikin kirsimeti tare da iyalinsa.

Sai dai kuma tangardar injin fitar da kudi na ATM ya sanya shi sauya tunanin yin bikin kisimetin tare da iyalin nasa.

Peter ya shaida wa BBC cewa tunda dai bai samu kudi ba, ba zai iya tunkarar iyalin nasa ba domin bai san mai zai fada musu ba.

Da alama ba masu son yin bukukuwan kirsimeti irin Peter ne kawai suka fuskanci matsalar samun kudi daga injin na ATM ba.

Akwai wadanda suke son yin amfani da kudade domin yin hutun sabuwar shekara kamar Muhammad Igab Salisu.

Shi ma Muhammad ya shaida wa BBC irin halin da injin na ATM ya jefa shi a ciki.

Bayanan bidiyo,

Muhammad Igab Salisu

Kusan za a iya cewa a duk lokacin da ake wasu bukukuwa a Najeriya ko hutu ko kuma lokacin biyan albashi, wata matsala da ke ci wa mutanen kasar tuwo a kwarya ita ce ta cire kudi daga injin ATM.

Lokacin irin wannan yanayi a kan ga jama'a na bin sahu kamar za su kada kuri'a.

Bayanan hoto,

Mutane sun yi layi a wurin ATM kamar suna zabe

Wani abun takaici ma shi ne yadda mutanen suke kwashe awoyi suna kan layi amma daga bisani suna komawa gidajensu ba tare da bukatarsu ta biya ba.

Wasu dai na danganta matsalar da rashin tsari irin na bankunan, a inda wasu kuma ke ganin tangardar na'urar ta ATM ce sila.

Bayanan hoto,

Mata da maza a kan layin ATM suna jira

Bayanan hoto,

Mata wasu da goyo wasu kuma sun zauna saboda gajiya

Bayanan hoto,

Mabiya layin ATM a Abuja