'Yan matan Chibok sun je gida kirsimeti

Za su yi bikin kirsimeti tare da iyalansu
Bayanan hoto,

'Yan matan Chibok sun sake ganawa da mahaifansu

'Yan matan nan guda 21 da kungiyar Boko Haram ta saki, sun isa garin Chibok na jihar Borno domin yin shagalin kirsimeti da iyalensu.

A watan Oktoban 2016 ne dai Boko Haram ta saki 'yan matan, bayan kwashe kusan shekaru biyu tana garkuwa da su.

Kuma wannan ne karo na biyu da 'yan matan suka sadu da 'yan uwa da iyaye a mahaifarsu tun bayan sako su.

Gwamnati dai ta kai 'yan matan wani boyayyen wuri domin tatsar bayanai daga wurinsu, bayan sakin nasu.

A watan Afrilun 2014 ne dai Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan matan su fiye da 270.

Har kawo yanzu kuma ana tsammanin fiye da 'yan matan 200 suna hannun kungiyar, a inda ake cigaba da tattaunawa kan sakin su.