Yadda bikin Kirsimeti ke hada kan al'umma a Nijar

lokacin yin addu'a ga kasa game da neman zaman lafiya
Bayanan hoto,

Kirsmeti na kawo hadin kai tsakanin kiristoci da musulmai a Nijar

Kamar sauran al'ummar Kiristoci a fadin duniya, a yau ne kiristoci a jumhuriyar Nijar, ke shagulgulan bikin Kirismeti, don tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

A jahar Damagaram ta jumhuriyar Nijar,kiristoci na zaune lami lafiya tare da 'yan uwansu musulmi.

A lokacin jin dadi ko kuma na bakin ciki su na murna tare ko kuma su jajantawa junansu.

Dangataka tsakanin Kiristoci da Musulmi ta kasance mai dogon tarihi,domin kiristoci sun shigo kasar ta Nijar ne, tun a shekarar 1024.

Tun kuma lokacin ne suke zaune lafiya a tsakaninsu.

A wannan lokaci na bikin kirismeti, kiristoci na gayyatar 'yan uwansu musulmi domin cin abinci da yin sauran shagulgula na jin dadi a tare.

Lokacin kirsimeti lokaci ne da al'ummar kirista a jumhuriya ta Nijar, ke amfani da shi domin yi wa kasa addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali baki daya .