Masifar son duniya ta ɓata ma'anar Kirsimeti —Paparoma

Paparoma

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Paparoma ya bukaci mutane su rika ƙaunar juna

Paparoma Francis ya ce masifar son duniya da mutane ke yi ta bata aihinin ma'anar bukukuwan Kirsimeti.

Paparoma ya bayyana haka ne a wajen addu'oin ranar Kirsimeti a fadarsa ta Vatican, inda aka tsaurara matakan tsaro.

Ya yi tur da yanayin da ƙananan yara ke ciki na uƙuba.

Shugaban Cocin Roman Katolikan ya ce kananan yara na fuskantar matsananciyar yunwa da hatsari da a kan hanyoyinsu na yin gudun hijira sakamakon harin bama-baman da ake ci gaba da kai wa a birnin Aleppo na kasar Syria.

Ya yi kira da a kawo karshen yakin da ake yi a kasar Syria.

Sai da aka caje mutanen da suka halarci wajen addu'oi tare da Paparoman kafin su shiga fadar tasa.

Asalin hoton, AFP

Asalin hoton, AP

Asalin hoton, Reuters

Paparoma ya ce, "Masifar da mutane suka dora wa kansu ta son duniya ta gurbata ma'anar bikin Kirsimeti", yana mai cewa ya kamata mutane su rika zama masu ƙan-ƙan da kai.

Asalin hoton, Reuters