'Yan bindiga sun kashe mutum 22 a DR Congo

Rikicin DR Congo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yankin Beni ya sha fama da rikici, inda mutane da dama suka rasa rayukansu

Hukumomi a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo sun ce 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 22 a Arewacin Kivu.

Sun daura alhakin kisan kan kungiyar masu ikirarin kishin Islama ta Uganda wato Allied Democratic Forces.

Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Beni a ranar Asabar.

Akwai rahotannin da ke cewa lamarin ya ritsa da wasu jama'a ciki har da sojojin Congo.

Ana sa ran adadin mutanen da suka mutu zai karu saboda rahotanni sun ce akwai gawarwaki da dama a cikin wani jeji da ke kusa da yankin.

Yankunan da ke makwaftaka da Beni sun sha fama da kashe-kashe inda daruruwan fararen hula suka rasa rayukansu a shekara biyu da ta gabata.