Kwankwaso ko Ganduje: Waye sahihin jagoran APC a Kano?

  • Mukhtar Adamu Bawa
  • BBC Hausa, Kano
Kwankwaso da Ganduje

Asalin hoton, Kano State Government

Bayanan hoto,

Kwankwaso da Ganduje sun shafe shekaru suna tafiya tare a siyasance

Wata wasika da shugaban jami'iyyar APC na Arewa maso Yamma ya aika, wacce ke goyon bayan Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar Kano, na tayar da jijiyoyin wuya tsakanin magoya bayan Gandujiyya da Kwankwasiyya.

Tuni dai tsagin kwankwasiyya ya yi watsi da takardar, wacce ta nemi Abdullahi Abbas na tsagin Gandujiyya ya ci gaba da rike shugabancin jam'iyyar a Kano.

Umar Haruna Doguwa na tsagin kwankwasiyya ya dage kan cewa har yanzu shi ne shugaban APC a Kano, don kuwa takardar ba umarnin uwar jam'iyyar ba ne.

Kimanin wata uku kenan ana jiran hukuncin uwar jam'iyyar tun bayan mika rahoton tantance gaskiya da ta aika Kano don sasanta rikicin da ke barazana ga cigaba da kasancewarta waje guda.

Rikicin ya balle ne sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma mutumin da ya gada, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Mutanen biyu sun shafe shekaru suna tafiya tare a siyasance kafin su babe a baya-bayan nan.

A cewar Doguwa, wani mutum ne zikau shi kadai ya rubuta wasikar.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya kara da cewa a matsayinsa na mamba a kwamitin zartarwar jam'iyya, kwamitin ne kadai yake da ikon sauke shi.

Tsugune ba ta kare ba

Sai dai mutumin da ya sanya hannu a takardar, Shugaban APC shiyyar Arewa maso Yamma, Inuwa Abdulkadir, ya shaida wa BBC cewa takardar ta dace da matsayin shugabannin jam'iyyar na yankin, wanda suka cimma a wani taro da suka yi a jihar Jigawa.

Shi ma Abdullahi Abbas ya ce umarnin da ke kunshe cikin takardar ya dace da tanadin tsarin mulkin jam'iyyar APC.

Takardar wadda aka yi ta yayata kwafenta a shafukan sada zumunta dauke da kwanan wata 12 ga watan Disamba ta ce taron na Jigawa ya nemi Abdullahi Abbas ya ci gaba da rike shugabancin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a zabi tabbataccen shugaba.

Sai dai Umar Haruna Doguwa ya ce ba abin da ya gudana kenan a taron Dutse ba, yana mai cewa akwai kusoshin jam'iyyar da dama wadanda ba a gayyace su zuwa taron ba.

Ana sa bangaren Abdullahi Abbas ya ce taron Jigawa ya samu halartar duk masu ruwa da tsaki wadanda suka tattauna kan kunshin rahoton Janar Magoro kuma suka amince da shi.

Har yanzu ga alama da sauran rina a kaba kan rikicin nuna fifiko a jam'iyyar APC ta Kano tsakanin bangaren da ake ganin yana tak'ama da k'arfin gwamnati da kuma tsagin masu ik'irarin goyon bayan rinjayen jama'a.