Zai yi wuya mu iya cimma Chelsea - Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce zai yi wuya kungiyar tasa ta iya cimma Chelsea wacce ke jan ragamar gasar a yanzu.

A yanzu City ce ta biyu a tebur bayan da ta lallasa Hull City da ci 3-0, inda ta ke bin Chelsea da maki bakwai.

A ranar Litinin ne Antonio Conte ya kafa sabon tarihi a Chelsea inda ya lashe wasanni 12 a jere bayan da suka doke Bournemouth da ci 3-0.

"Mun yi wasanni bakwai fiye da Chelsea, kuma wannan shi ne abin da ke ba mu wahala," a cewar Guardiola.

"Saura kiris Liverpool ta lashe gasar a wata shekara saboda ita kadai ce gasar da suka saka a gaba, haka itama Leicester, abin da ya faru da ita kenan bara.

"A wannan karon Chelsea da Liverpool ne ke da wannan damar."

Duka Liverpool da Chelsea ba su samu damar shiga gasar zakarun Turai ba bayan da suka kare a mataki na takwas da goma a kakar da ta gabata.