Turkiyya: An gurfanar da 'yan sanda a kotu kan juyin mulki

Jami'an 'yan sanda 29 ne aka gurfanar a kotu

Asalin hoton, AFP

An gurfanar da jami'an 'yan sanda 29 a birnin Istanbul na Turkiyya inda aka tuhume su da hannu a yunkurin kifar da gwawmnatin Shugaba Racep Tayyip Erdogan a watan Yuli.

Wannan dai ita ce shari'a mafi muhimmanci da aka fara yi wa wadanda ake zargi da juyin mulkin, baya ga wasu 'yan kananan shari'o'i da ake gudanarwa a fadin kasar.

Hukumomin kasar dai sun tanadi dubban hujjoji kan mutanen da ake zargi.

Mutum 40,000 ne ake tsare da su bisa zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Racep Tayyip Erdogan, kuma ana ganin shari'ar za ta zama mafi girma a tarihin kasar.

Baya ga zargin yunkurin juyin mulki, ana kuma zargin mutanen da kasancewa 'yan kungiyar malamin nan na Turkiya da ke zaune a Amurka Fethullah Gulen, mutumin da hukumomi suka zarga da kitsa juyin mulkin.

Sai dai malamin ya musanta zargin.

An fara shari'ar ta kwanaki hudu ne ranar Talata a wani gidan yari da ke bayan garin Istanbul, karkashin tsauraran matakan tsaro.

Ashirin da daya daga cikin 'yan sandan na fuskantar daurin rai da rai idan an same su da laifi, ciki har da gazawa wajen kare shugaban kasa.

Sauran takwas din kuma suna fuskantar kananan tuhume-tuhume.