A bai wa Chelsea kofi a huta - Savage

'Yan wasan Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan wasan Wales kuma mai yi wa BBC sharhi kan kawallon kafa, Robbie Savage, ya ce kamata ya yi a bai wa Chelsea kofin Premier kawai domin babu wanda zai iya cimmu su.

A yanzu Chelsea ta bayar da tazarar maki bakwai ga Manchester City, yayin da aka kusan kammala rabin kakar wasa ta bana.

Da yake magana a shirin BBC Radio 5 Live bayan nasarar da Chelsea ta samu a kan Bournemouth, wanda shi ne wasa na 12 da suka lashe a jere, Savage ya ce ba ya ganin akwai wani kulob da zai iya kawo cikas ga tawagar ta Antonio Conte.

"Kawai a basu kofi tun yanzu a huta - Ba na ganin akwai wanda zai iya kamo su," a cewarsa.

"Suna da 'yan baya, ga kwararrun 'yan gaba. Za su iya yin kowanne irin salon wasa; za su iya yin kaca-kaca da abokan hamayyarsu".

Tsohon dan wasan na Wales ya kara da cewa Chelsea sun samu nasara kan kungiyoyi irinsu West Brom, wadanda ke tarewa a gida domin ganin ba a zira musu kwallo ba, amma kuma sun samu nasara duk da haka.

Idan Chelsea ta doke Stoke a karshen makon nan, to za su iya cimma tarihin da Arsenal ta kafa na lashe wasa 14 a jere a 2002 a lokacin da za su kara da Tottenham a White Hart a ranar 4 ga watan Janairu.