India: An yi wa 'yar Amurka fyade da kwaya a Delhi

Fyade ya zama ruwan dare a kasar India

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

zanga-zangar mata kan kin jinin fyade a India

'Yan sanda a Delhi, babban birnin kasar India, sun kama wasu maza hudu da ake tuhuma da saka wa wata 'yar yawon bude ido Ba-Amurkiyya kwaya da manufar yi mata fyade.

Tun dai watan Afrilun da ya gabata ne al'amarin ya faru amma kuma sai a farkon watan Disamba matar ta koma India domin bayar da bahasi kan abun da ya faru da ita.

Ta kuma sanar da cewa, ta na zaune a wani otal sai mai yi mata hidima ya saka mata kwaya, a inda wasu maza hudu su ka yi lalata da ita.

Mazan hudu da ake tuhuma sun hada da mai kula da yi wa matar hidima a otal din da direba da mai shara da kuma wani ma'aikacin otel din.

Wannan dai shi lamari na baya-baya irinsa da ya faru ga mata 'yan kasashen waje da ke yin balaguro a kasar ta India.

Hukumomi dai na yin iya kokarinsu wajen dakusar da lamarin fyade ga mata da ke kokarin zama ruwan dare a kasar ta India.