Ziyarar 'yan matan Chibok ta bar baya da kura

'Yan matan Chibok sun sake ganawa da mahaifansu
Wasu iyayen `yan matan wadanda suka nemi a sakaya sunansu sun ce ba a ba su damar ganawa da 'ya'yan nasu ba cikin walwala.
Wani mahaifi ya ce ya dauki hoton da 'yarsa, amma sai wani jami'in tsaro ya kwace wayar ya ce sai ya goge hoton, "duk kuwa da na ce masa 'yata ce na dauki hoton da ita."
Ya yi zargin cewa jami'in tsaron ya goge gaba-daya hotunan da ke cikin wayar har ma da wadanda ba a nan aka dauke su ba.
An dai kai 'yan matan ne gidan wani dan majalisar dokoki na yankin domin su gana da iyayensu, sai dai rahotanni sun ce an hana su zuwa gidanjensu.
Wani mahaifin daban kuma cewa ya yi "ni ban amince cewa 'yata ta zo kusa da gida haka ba, 'yan uwanta da dama ba su gan ta ba tun lokacin da aka sace su, kuma har yanzu suna kokwanton ko ma an kubutar da ita".
Ya ce babu dalilin da za a kawo su Chibok a kuma tsare su a wani kurkukun, domin ko coci ba su je ba ranar Kirsimeti.
Ita ma wata uwa ta ce "na yi matukar mamaki a ce 'yata ba za ta iya zuwa gida ba, ban ga abin da zai sa ni farin ciki ba, domin kuwa har yanzu 'yata ba ta samu 'yanci ba."
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Iyayen 'yan matan nan na Chibok 21 da suka yi bukukuwan Kirsimeti a gida sun shaida wa BBC cewa ba su ji dadin yadda aka tsara ziyarar ba.
To sai dai a bangarenta, gwwamnatin kasar ta ce ta samu labarin abinda jami'an tsarin suka yi, kuma ta yi takaicin abinda wasu jami'an tsaron suka yi na tsananatawa.
Mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari na musamman kan hulda jama'a Malam Garba Shehu ya shedawa BBC cewa lamarin ya faru ne, sakamakon rashin fahimtar wasu jami'an tsaro kan manufar gwamnati na kai 'yan matan Chibok domin bukukuwan kirsimeti.
Malam Garba ya ce mahukunta sun yiwa tufkar hanci, amma ya ce dole ne suma jama'a su fahimci cewa batu ne na tsaro wanda dole sai an yi taka-tsan-tsan.
Hukummomi tsaron Nigeria ne dai suka kai 'yan matan guda 21 da kungiyar Boko Haram ta saki garin Chibok na jihar Borno domin yin shagalin kirsimeti da iyalensu.
A watan Oktoban 2016 ne Boko Haram ta saki 'yan matan, bayan kwashe kusan shekaru biyu tana garkuwa da su.
Kuma wannan ne karo na biyu da 'yan matan suka sadu da 'yan uwa da iyaye a mahaifarsu tun bayan sako su.
Gwamnati dai ta kai 'yan matan wani boyayyen wuri domin kula da su da kuma samun bayanai daga wurinsu, bayan sakin nasu.
A watan Afrilun 2014 ne dai Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan matan su fiye da 270, kuma har yanzu mafi yawansu na can a hannun kungiyar.
Har kawo yanzu kuma ana tsammanin fiye da 'yan matan 200 suna hannun kungiyar, a inda ake cigaba da tattaunawa kan sakin su.